کاربر:Hassan
Lauhul mahawi wal isbat (Larabci: الگو:Arabic) wani allo ne wanda ake rubuta duk abubuwan da za su faru a duniya, amma yana iya canzawa. Malaman tafsiri sun yi bayani qarqashin a aya ta 39 a cikin suratul ra'ad cewa, abubuwan da suke faru a duniya ana rubuta tuntuni an rigaya an rubuta su cikin lauhul mahfuz wanda ake kiyaye abubuwa a yanayin da ɗari bisa ɗari za su faru, sannan kuma a cikin allan gogewa da tabbatarwa,wato shi allu iri biyu ne, da wanda abubuwa suke canzawa da kuma wanda har abada basa canzawa, saboda haka duk abin da za'a rubuta a cikin allu na gogewa da tabbatarwa yana iya ya canza, kuma shi wannan allu na gogewa da tabbatarwa ɗaya ne daga cikin matakan ilimi Allah,kuma mu ba musa haƙiƙanin yadda yake ba, kai annabawa da imamai ne suka san yadda yake.
Canje-canjen da ke faruwa a cikin allun gogewa da tabbatarwa Allah ya san dasu suna cikin iliminshi marar iyaka,saboda haka duk wani canji da zai faru yana cikin ilimin Allah marar iyaka, saboda haka dan ansami canji a allan gogewa da tabbatarwa baya nufin cewa ansami canji a cikin ilimin Allah,saboda abin da ya zo a cikin hadisai cewa wasu ayyuka, kamar sadaka, da sada zuminci,da addu'a na iya kawo sauyi a allan gogewa da tabbatarwa. A cewar masu bincike, allann gogewa da tabbatarwa da canjin da yake faruwa yana da da fa'idoji, kamar neman ɗan adam ya canza makomarsa shi, mumini ya rayu cikin tsoro da fata, kuma muminai ta hanyar labaran annabawa su san tasirin kyawawan ayyuka da munanan ayyuka ga ayyukansu.
Muhimmancin wannan Maudu'i a wajan bincike a musulinci Allan Gogewa da tabbarwa yana nuni da samuwar wani matakin ilimi na Ubangiji wanda a cikinsa ake rubuta abubuwan da suka faru a duniya [1] kuma an faɗa a cikin litattafan tafsiri ta hanyar amfani da faɗar Allah maɗaukaki cewa, «يَمْحُو اللَّهُ مَا يَشَاء وَيُثْبِتُ وَعِندَهُ أُمُّ الْكِتَابِ»[٢ ma'ana Allah yana goge abin da Yake so kuma yana tabbatar da abin da yaso kuma a gunshi ne littafin ƙarshe wanda ya ƙunshi komai yake.haƙiƙa duk abin da yake faruwa a duniya an rubutasu a cikin alluna guda biyu mabanbanta,na ɗaya shin Lauhil Mahfuz, na biyu kuma shi ne Lauhil Mahwo Wal'isbat.[3] Abin da aka rubuta a cikin allun gogewa da tabbatarwa yana iya canzawa, amma abin da aka rubuta a cikin lauhil mahafuz, ba zai canza ba. Domin abin da aka rubuta a cikin Allunan Gogewa da tabbatarwa, kamar dalilai ne da ba su cika ba (wani dalili ne da ba a tabbatar da shi ba),amma abubuwan da aka rubuta a cikin lauhil mahfuz suna da cikakkun sababi da dalili (tabbatacen dalili)[4].
Malami al-Majlisi, marubucin littafin Bihar al-Anwar, ya ambaci cewa, kalmar allunan gogewa da tabbatarwa an samushi ne daga ayoyi da ruwayoyi[5].a bangare ɗaya kuma wasu naganin cewa wannan kalma ta allan gogewa da tabbatarwa bata da a asali daga Kur'ani ko ruwaya, sai dai cewa wannan Isɗilahi anjishi ne a farko ta wurinAllamal Majalis, [6]. Ta haka ne Allah Ta'ala ba shi da wani allu mai zaman kanshi da ake kira da Allun Gogewa da tabbatarwa, sai dai gogewa da tabbatarwa suna faruwa ne a cikin Lauhil Mahfuz (Ummul Kitab)[7].
Ana daukar allun gogewa da tabbatarwa a matsayin bayyana da cikakken ikon Allah madaukaki[8]. , amma ba su san abin da ke cikin Allunan da aka kiyaye ba [9] A cewar masu ilimi aƙida, Mala'ika da annabawa da imamai basu san abin da zai faru a gaba ba, sai ta hanyar allun gogewa da tabbatarwa wanda yake iya canzawa,amma kuma ba su san abin da yake cikin Lauhil Mahfuz ba.[9] bisa abin da masu bincike sukace, mu bamu da masaniya kan allun gogewa da tabbatarwa, kuma bai kamataba a kamantashi ba da litattafai namu na yau da kullin ba.[10] Amma Faidil Kashani mawallafin tafsirul Safi yana ganin , kan wannan matsala ta allun gogewa da tabbatarwa da kuma lauhil mahfuz cewa, duk abubuwa da suke a duniya ana rubutasu a dunƙule a cikin wani allu na ƙada'a wanda yake shi ne Lauhil Mahfuz, sanna kuma sai a rubutasu a allu na ƙadar amma filla-filla, wannan shi kuma shi ne allu na gogewa da tabbatarwa.[11]
Ba bu karo tsakanin canjin da yake farowa a allo na goge abubuwa da tabbatar da su da kuma ilimin Allah.
Malaman Musulunci ba su yi imani da cewa canji da yake farowa a allan gogewa da tabbatarwa yana nufin canji a cikin ilimin Allah Madaukakin Sarki[12]. Wasu asu bincike suna ganin akwai matsala kan canji da yake farowa a allan gogewa da tabbatarwa,sna cewa wannnan canji ƙila yana nufin cewa Allah Ta'ala bai san canja-canjan da suke farowa ba kan abubuwan da ke faruwa a duniya ba. [13]. Sai suka amsa da ewa wannan canji da da ke faruwa a cikin allan gogewa da tabbatarwa su ma suna nan a cikin ilmin Allah mara iyaka, [14] Kuma Allah maɗaukakin sarki ba ya sanar da waɗannan canje-canje sai a cikin abubuwa da ba sa bayyana niyarshi da bata canzawa.[15]
Kamar yadda wasu masu bincike suka yi nuni da cewa, sabanin Ahlus-Sunnah da ‘yan Shi'a dangane da mas'alar badi'a (bayyanar wani abu daga Allah Madaukakin Sarki wanda ya saba wa abin da bayinshi suke tsammani) abu ne da bashi da muhimmaci. Domin Ahlussunnah suma sun yarda da allan gogewa da tabbatarwa kamar ‘yan Shi'a, amma aƙidar Bada'a, ita ce imani da allan gogewa da tabbatarwa, kuma ta aƙidar Badaa'a wacce take cikin aƙidun Shi'a, bata faruwa sai a cikin allan gogewa da tabbatarwa.[16].
Ta fuskacin Falsafa [himar hakan]
Mullah Sadra, wanda ya assasa makarantar falsafa ta hikima Almuta'aliya Alfalsafiyya yana gabatar da cikakken ɗan adam ta fuskar tinaninshi, a matsayin Allauhil Mahfuz, da kuma ta fuskar abu mai kama da dabba (wanda yake da Kayali) a matsayin allan gogewa da tabbatarwa. [17] kamar yadda malama Faid Al-kashani, ɗaya daga cikin daliban Mullah Sadra, shi ma ya yi amfani da Allauhil Mahfuz idan ya ɗabbaƙa duniyar tinani da hankali kan Allauhil Mahfuz,shi kuma Allu na gogewa da tabbatarwa akan duniyar ta ran ɗan adam. [18].Amma Mulla Sadra yana ganin koyi da Muhyiddin Binin Arabi cewa,shi allan gogewa shi ne gurin da shari'a take bubbugowa da kuma dukkan litattafan da Allah yake turowa daga sama, saboda haka ake goge shari'a da hukunce-hukunce[19]. Sai daai cewa wasu masu bincike sun ce ba dai-dai bane a ɗabbaƙa abubuwan da suke na ankali kan allan gogewa da tabbatarwa [20].
Abubuwan da suke sa Lauhil Mahwo Wal Isbat ya canza
Duk wani aiki mai kyau ko mara kyau yana iya haifar da canji a cikin allo na gogewa da tabbatarwa[21]. Kuma ya zo a cikin Alƙur'ani da hadisi wasu daga cikin ayyuka da suke sa caanji a cikin allo na gogewa da tabbatarwa mafi muhimmanci ita ce shi ne tasirin addu'a da sadaka da sada zumunci[22] kamar yadda wasu ruwayoyi suka nuna, addu'a na iya mayar da wata ƙaddara mai ƙarfi. [23]. Kuma an ambaci irin rawar da sadaka ke takawa wajen kawar da mutuwa marar kyau, da san tsawaita rayuwa, da kore fatara duk wannan a cikin hadisai[24].kuma ya zo a cikin wani hadisi daga annabi amincin Allah ya tabbata a gareshi cewa, sada zumunci yana haifar garuwar arziƙi da tsawaita
rayuwa[25].
Amfanin Lauhul Mahwo wal Isbat
Wasu masu bincike sun jera fa'idodi masu zuwa na allon gogewa da tabbatarwa [Al-bada'a]
- Mumini yana rayuwa cikin tsoro da fata [26].
- Muminai su san tasirin kyawawan ayyuka da munanan ayyukansu ta hanyar labarin da Annabawa suak kawo musu [27].
- Bayanin banbance tsakanin ilimin mahalicci da ilimi halittu[28].
- tsananin nauyin da ya hau kansu da kuma tsananin jarrabawa kan muminai Tsarkake wajibai da fitintinu a kan muminai, ta yadda za su sami domin idan suka daurewa hakan Allah zai basu lada da yawa lada mai yawa[29].
- ɗan adam ya yi ƙoƙari wajan canza makomarshi[30].